Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci 'yan majalissar Amurka da su kauracewa goyon bayan masu tsattsuran ra'ayi na Hong Kong
2019-08-13 20:41:06        cri

Kakakin ofishin kwamishina a ma'aikatar harkokin wajen Sin dake yankin Hong Kong, ya soki lamirin wasu 'yan majalissun dokoki kasar Amurka, bisa zargin da suke yi wa gwamnatin tsakiyar kasar Sin da gwamnatin yankin ba tare da wata hujja ba, yana mai kira gare su da su tsame hannuwansu, daga goyon bayan ayyukan tsageru masu tsattsauran ra'ayi a yankin na Hong Kong.

Jami'in dai ya yi wannan tsokaci ne a matsayin martani, bayan da aka rawaito shugaban masu rinjaye a majalissar dokokin Amurkan daga jam'iyyar Republican Mitch McConnell, na cewa gwamnatin tsakiyar kasar Sin na kokarin danne hakkin yankin Hong Kong na kasancewa mai cin gashin kai, da ma 'yancin walwalar al'ummar sa. McConnell ya ce ba za a taba amincewa da kokarin yiwa yankin danniya ba.

Game da hakan, cikin wani sako da aka wallafa ta shafin yanar gizo, kakakin ofishin kwamishinan, ya ce kalaman dan majalissar Amurkan sun kaucewa gaskiya, suna kuma kunshe da zargi maras tushe ga gwamnatin tsakiyar Sin, da ma mahukuntan yankin na Hong Kong, wanda hakan ka iya aikewa da mummunan sako ga masu tarzoma. Ya ce Sin tana adawa, ta kuma yi watsi da wannan zargi.

Jami'in ya kara da cewa, wasu 'yan tsiraru cikin masu zanga-zanga a yankin Hong Kong, sun aikata abubuwa na wuce iyaka, da tada zaune tsaye, suna rika cin zarafin 'yan sanda, da jifan su da abubuwa masu hadari cikin yanayi mai muni. Ko shakka babu irin wannan hali ya sabawa dokokin zamantakewar, ya kuma haifar da barazana ga tsaron al'umma. Kaza lika hakan ya zama wani babban kalubale ga zaman lumana a Hong Kong, ya kuma keta hurumin kasa daya tsarin mulki biyu da ake aiwatarwa.

Kakakin ya kuma jaddada cewa, yankin Hong Kong bangare ne na Sin, kuma duk wani batu na yankin harka ce ta cikin gidan kasar Sin, wanda ba ya bukatar tsoma hannun wata kasa ta waje, ko wata kungiya ko daidaikun mutane ta ko wace siga.

Daga nan sai ya bayyana cewa, bai dace wani ya taba zaton zai dakile aniyar kasar Sin game da kare ikon mulkin kanta, da tsaron kanta, da samar da wadata da kwanciyar hankali a yankin na Hong Kong ba. Kaza lika kada wani ya zata cewa Sin za ta ba da kai ga barazana, ko wani matsin lamba daga wasu yankunan dake ketare.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China