Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kama masu tarzoma 149 a Hong Kong
2019-08-12 20:09:09        cri

A yammacin ranar 12 ga wata, hukumar 'yan sandan yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, ta shirya taron manema labaru a hedkwatarta dake Wan Chai, inda aka yi nuni da cewa, kwanan baya an kara tayar da hankali a Hong Kong, inda masu tarzoma suka kara nuna karfin tuwo. Wadannan 'yan daba ba su girmama dokoki ba, inda suka yi abun da suka ga dama, wajen ta da tarzoma a Hong Kong, tare da haifar da barazana ga tsaron mazauna yankin. Don haka daga ranar 9 zuwa 12 ga watan nan, 'yan sandan sun kama masu tarzoma 149. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China