Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina tsoma baki a harkokin yankin Hong Kong
2019-08-13 10:56:23        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bukaci Amurka da ta gaggauta daina tsoma baki a harkokin cikin gidan yankin musamman na Hong Kong. Kalaman Madam Hua na zuwa ne, yayin da take mayar da martani game da yadda a 'yan kwanakin nan ake kokarin mayar da yankin tamkar wani fagen juyin juya hali.

Hua ta ce, Amurka ta sha furta kalaman da ba su dace ba a kan yankin na Hong Kong, inda aka kasa fahimta tsakanin fari da baki da ma ingiza tashin hankali. Ta ce wasu 'yan siyasa da jami'an diflomasiyar Amurka da suka gana da masu tayar da boren, sun zargi gwamnatin tsakiyar kasar Sin ba tare da wata hujja ba, suka shirya makarkashin tayar da hankali da ayyukan illata makoma da ma zaman lafiyar yankin na Hong Kong.

Amma duk da wadannan munanan abubuwa, jami'ar na mamakin, shin mene ne hakikanin manufar Amurka, da dalilinta na yin amfani da yankin Hong Kong.

Don haka, Madam Hua ta sake nanata cewa, Hong Kong, wani bangare ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba, kuma harkokin yankin Hong Kong, batu ne da ya shafi harkokin cikin gidan kasar Sin. Kasar Sin tana kira ga Amurka da ta mutunta dokokin kasa da kasa da muhimman ka'idojin akalar kasa da kasa, ta kuma gaggauta daina tsoma baki a harkokin cikin gidan kasarta.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China