Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi jinping: za a hada kai wajen samar da makoma mai haske kan muhallin halittun duniya
2019-08-19 15:27:31        cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya mikawa taron dandalin lambunan shan iska na kasa karo na farko wasikar taya murnar budewa, tare da maraba ga wadanda suka halarci taron daga kasashe daban-daban.

A cikin wasikar, Xi Jinping ya jaddada cewa, tilas ne Sin ta kara karfin kiyaye muhallin hallitu, kuma ya kamata ta yi la'akari da halin da Sin take ciki yanzu, tare da koyon fasahohi daga kasashen waje. Ya ce, yana fatan za a tattauna sosai bisa taken "Kafa wani tsarin kiyaye muhalli bisa tushen lambun shan iska na kasa", ta yadda za a ba da gudunmawa wajen samar da makoma mai haske kan muhallin hallitu, da kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'Adama. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China