Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya karfafa gwiwar mazauna kauyen Xiadang da su yi kokarin farfado da wurinsu
2019-08-06 15:47:40        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta wasika ga mazauna kauyen Xiadang na gundumar Shouning dake lardin Fujian na kasar Sin, yana mai basu amsar sakon su, inda ya taya su murnar cimma burin kawar da talauci, kana ya kara musu kwarin gwiwar ci gaba da kokari da nufin farfado da kauyensu.

A yayin da Xi Jinping ke aiki a lardin Fujian, ya taba zuwa garin Xiadang har sau uku, don yin bincike, da ba da jagoranci kan aikin kawar da talauci. A 'yan kwanakin da suka wuce, a madadin mazauna kauyen, wasu 'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na garin Xiadang su shida, sun rubuta wasika ga shugaba Xi Jinping, don gaya masa labari mai kyau game da kawar da talauci a kauyensu, tare kuma da nuna godiya ga kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis na kasar da kuma shugaban kasar. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China