Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya jaddada muhimmancin maida hankali kan gyare-gyare domin karfafa rundunar sojin kasar
2019-07-31 20:12:26        cri
Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin zage damtse wajen aiwatar da gyare-gyare don karfafa rundunar sojojin kasar, ta yadda za ta daga matsayin ta, har ta kai ga zama runduna mai karfi a sabon zamani da ake ciki.

Xi ya yi wannan kira ne a jiya Talata, yayin da yake jagorantar zaman nazarin ayyukan da suka shafi gudanar da gyare-gyare ga rundunar sojojin kasar ta Sin, da sauran hukumomin rundunar, wanda ofishin hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS ya shirya.

Yayin zaman, wanda ya gudana gabanin ranar sojoji ta kasar Sin dake tafe a ranar 1 ga watan Agusta, a madadin kwamitin kolin JKS, da hukumar rundunar sojojin kasar, shugaba Xi ya gabatar da gaisuwar sa ga daukacin jami'an rundunar sojojin kasar ta PLA, da 'yan sanda masu dauke da makamai, da jami'an da ake tanada domin ayyukan ko ta kwana. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China