Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya ba da umarni a gudanar da aikin ceto a birnin Guizhou yadda ya kamata
2019-07-24 20:21:45        cri

Jiya da misali karfi 9 da mintoci 20 na dare agogon wurin, an samu gocewar kasa a gundumar Shuicheng na birnin Liupanshui dake lardin Guizhou, lamarin da ya binne gine-gine 21, ya zuwa yanzu mutane 11 sun mutu, wasu 42 kuma ba a ji duriyarsu ba.

Bayan aukuwar wannan bala'i, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dora muhimmanci sosai kan lamarin, ya kuma ba da muhimmin umarni, inda ya bukaci a yi kokarin gano tare da ceto wadanda suka makale a karkashin kasa, a ba da jinyya ga wadanda suka jikkata tare da tsugunar da wadanda bala'in ya shafa, kana a kula da iyalan mamata da sauran ayyuka. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China