Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron CPC ya tattauna batun yanayin tattalin arziki
2019-07-30 19:23:22        cri

Ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya gudanar da taro a jiya Talata, domin duba yanayin tattalin arziki, da tsare tsaren gudanar sa a watanni 6 na biyu na shekarar nan da muke ciki. Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, shi ne ya jagoranci zaman taron.

Wata sanarwa da aka fitar bayan taron, ta ce tattalin arzikin Sin na samun ci gaba cikin daidaito a wadannan watanni 6 na farkon shekarar 2019.

Kaza lika taron ya yi kira da a aiwatar da dukkanin matakan da suka wajaba, domin tabbatar da daidaiton ci gaban da aka samu, a kuma ci gaba da sauye sauye, da kara kyautata rayuwar al'umma. Kaza lika a dakile hadurra, da wanzar da ci gaba mai dorewa a fannin ci gaban tattalin arzikin kasar ta Sin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China