Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya aikawa takwaransa na Masar sakon ta'aziyya dangane da harin ta'addancin da aka kai Alkahira
2019-08-07 19:17:58        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikawa takwaransa na kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi sakon ta'aziyya dangane da harin ta'addanci na baya-bayan da aka kai birnin Alkahira, fadar mulkin kasar Masar.

A cikin sakon, Xi ya ce, ya kadu a lokacin da ya samu labarin harin ta'addancin da aka kai a birnin Alkahira, inda mutane da dama suka jikkata.

A madadin gwamnatin kasar Sin da jama'arta, da ma shi kansa, Xi, yana mika sakon ta'aziyya dangane da wadanda harin ya rusa da su, da jajantawa wadanda suka jikkata da ma iyalansu, tare da fatan wadanda suka jikkata za su samu sauki cikin sauri.

Shugaban na Sin ya kuma bayyana cewa, kasarsa tana adawa da duk wani nau'i na ta'addanci, kana ta yi matukar yin Allah wadai da harin, yana mai cewa, kasar Sin tana goyon bayan matakan da Masar take dauka a kokarin da take na tabbatar da tsaro da zaman lafiya da ma yaki da ayyukan ta'addanci.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China