Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Kasashen waje su daina ingiza masu tayar da bore a Hong Kong
2019-08-06 20:08:44        cri

Game da mummunar sanarwar da shugabar majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi ta fitar a yau Talata, kakakin ofishin wakilin musamman na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin dake yankin musamman na Hong Kong ya bayyana cewa, kasar Sin ta nuna matukar Allah wadai tare da nuna adawa da matakin Nancy Pelosi na goyon bayan masu tsattsauran ra'ayi da su tayar boren da ya sabawa doka, da yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan Hong Kong da na kasar Sin.

Kakakin ya kara da cewa, tun bayan da yankin Hong Kong ya dawo karkashin ikon kasar Sin shekaru 22 da suka gabata, ana aiwatar da tsarin nan na "kasa daya, amma tsarin mulki biyu", kuma 'yan Hong Kong ne ke gudanar da harkokin yankin da kansu cikin 'yanci yadda ya kamata, 'yan Hong Kong na tafiyar da harkokinsu bisa 'yanci kamar yadda doka ta tanada. Amma, 'yan siyasar Amurka kamar Nancy Pelosi sun mai da fari baki kuma sun kasa gane tsakanin karya da gaskiya, suna danne gaskiya da nufin tada zaune tsaye a Hong Kong, matakin da ya bayyana mummunan burinsu na kawo cikas ga Hong Kong da dakile babban yankin kasar Sin.

Kazalika, kakakin ya jaddada cewa, harkokin yankin Hong Kong harkokin cikin gidan kasar Sin ne. Don haka ya bukaci 'yan siyasar Amurka da su daina zuga masu tsattsauran ra'ayi suna tayar da bore a yankin, su kuma dakatar da sa kaimi ga daftarin dake da alaka da yankin Hong Kong, su daina tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Hong Kong da na kasar Sin nan da nan. Idan ba haka ba, 'yan Hong Kong da daukacin jama'ar kasar Sin za su bayyana matukar rashin jin dadi su kuma mayar da martani. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China