Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin gwamnatin tsakiyar kasar Sin ya yi tir da harin masu zanga-zanga kan 'yan sandan Hong Kong
2019-08-12 20:00:30        cri

Mai magana da yawun ofishin majalissar gudanarwar gwamnatin tsakiyar kasar Sin game da yankunan Hong Kong da Macau Yang Guang, ya yi tir da harin da masu zanga-zanga suka kaddamar kan 'yan sandan Hong Kong.

Yang Guang ya yi Allah wadai da mummunan aikin harba bam da aka hada da fetur kan 'yan sanda, wanda hakan ya haifar da jikkatar wasu daga jami'an 'yan sandan yankin.

Ya ce, "muna matukar nuna bacin ranmu, da Allah wadai bisa wannan danyen aiki, kuma mummunan laifi da aka aikata". A hannu guda kuma ya yi fatan samun sauki ga 'yan sandan da suka ji raunuka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China