Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in Iran: Ta'addanci irin na tattalin arziki da Amurka ta aiwatar ya ci tura
2019-08-16 15:35:13        cri
Mahukuntan Gibraltar mallakar Britaniya, sun yanke shawarar sakin jirgin ruwa mai suna "Grace 1" da suka tsare, wanda ke dauke da danyen man Iran a jiya Alhamis. Bayan hakan, ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya ce, ta'addanci iri na tattalin arziki da Amurka ta aiwatar kan kasar Iran ya ci tura.

Mohammad Javad Zarif ya bayyana a kan Intanet a wannan rana cewa, Amurka ba za ta cimma burinta ba ta aiwatar da irin wannan mataki, hakan ya sa tana nufin amfani da doka da shari'a yadda take so, don kwace dukiyar Iran a haddin ruwan tekun jama'a, lamarin da ya bayyana cewa, gwamnatin Donald Trump ba ta mutunta shari'a da doka ko kadan.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya ya nuna a wannan rana cewa, Birtaniya ta gano cewa, mahukuntan Gibraltar sun sami takardar shaidu daga bangaren Iran dake bayyana cewa jirgin ruwan ba kasar Sham zai tafi ba. Kakakin na neman Iran ta cika alkawarinta, ya ce, Birtaniya ba za ta amince Iran ko daidaikun mutane su yi jigilar man fetur zuwa Sham ba, domin matakin ya keta takunkumin da EU ta kakkabawa kasar Sham. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China