Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe mambobin hukumar zartaswa ta IAEA sun yi kira da a kiyaye yarjejeniyar nukiliyar Iran a dukkanin fannoni
2019-07-11 13:38:24        cri

Kasashe mambobin hukumar zartaswa a hukumar lura da makamashin nukilya ta kasa da kasa wato IAEA, sun kira wani taro na musamman a jiya Laraba a birnin Vienna, don tattaunawa kan yadda Iran ta gudanar da yarjejeniyar nukiliyarta a duk fannoni, da dai sauran abubuwa masu nasaba da hakan.

Kasashen Sin, Amurka, Rasha, Birtaniya, Faransa da Jamus da dai sauran mambobi kasashe 35 sun halarci taron, inda wakilan Iran da EU, da dai sauransu suka gabatar da jawabai. Shugaban hukuma mai kula da harkokin jan damara ta kasar Sin Fu Cong, ya jagoranci tawagar kasar Sin wajen taron.

An gudanar da wannan taro ne dai bisa rokon Amurka, kuma yawancin kasashe mambobin IAEA sun amince da kiyaye wannan yarjejeniya, da nuna matukar rashin jin dadi kan janyewar Amurka daga yarjejeniyar. A sa'i daya kuma, sun yi kira ga Iran, da ta cika alkawarinta, tare da goyon bayan kokarin diplomasiyya da kasashe masu ruwa da tsaki suka yi na kiyaye ta. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China