Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Iran ya yi watsi da takunkumin da Amurka ta sanya masa
2019-08-01 16:02:49        cri
Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya yi fatali da matakin da Amurka ta dauka na sanya masa takunkumai.

A cewar hukumar adana kudaden Amurka, dukkan wasu kaddarori mallakin Zarif dake jihohin Amurka ko kuma suke karkashin ikon jami'an Amurka, dole ne a kame su kuma a mika su ga gwamnatin Amurkar.

Bugu da kari, duk wata hukumar dake gudanar da harkokin kudade wadanda ke da alaka ko kuma ake gudanar da su a madadin Zarif za su fuskanci hukunci daga gwamnatin Amurka. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China