Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen dake cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran sun sake tabbatar da kudurinsu game da yarjejeniyar
2019-07-29 10:19:48        cri

Kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran, sun nanata kudurinsu ga yarjejeniyar tare da sukar Amurka bisa kakaba takunkumi bisa radin kanta, a yayin taron da suka yi jiya Lahadi a birnin Vienna na Austria.

Wakilin kasar Sin Fu Cong, wanda kuma shi ne darakta janar na sashen kula da takaita yaduwar makamai na ma'aikatar harkokin wajen Sin, ya bayyana yayin taron manema labarai da aka yi bayan taron cewa, akwai sakonni biyu da taron ya samar.

Ya ce sako na farko shi ne, dukkan bangarorin dake cikin yarjejeniyar, sun bayyana kudurinsu na kare ta, tare da ci gaba da aiwatar da kunshinta bisa sahihin yanayi da adalci.

Na biyu kuma shi ne, dukkan bangarorin sun bayyana adawarsu da matakin Amurka na yin gaban kanta wajen kakaba wa Iran takunkumi, musammam fadada takunkumin fiye da iyakarta. Sannan sun bayyana goyon baya da godiyarsu ga kokarin kasar Sin na aiwatar da yarjejniyar, musammam kokarinta na ci gaba da gudanar da cinikayya da dangantakar man fetur tsakaninta da Iran.

Babban mai kula da yarjejeniyar na kasar Iran, Abbas Araqchi ya bayyana taron a matsayin mai ma'ana.

A cewar wasu majiyoyin diflomasiyya dake Vienna, an gudanar da taron ne bisa bukatar kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya da Iran, domin nazarin batutuwan dake da alaka da aiwatar da dukkan bangarorin yarjejeniyar. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China