Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jagoran addini na kasar Iran ya mayar da martani game da kwace jirgin dakon man kasar da Birtaniya ta yi
2019-07-17 10:57:04        cri
Jagoran addini na kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce ba za a kyale batun kwace jirgin dakon man kasarsa da Birtaniya ta yi ba bisa ka'ida ba.

Gidan talabijin na kasar ya ruwaito Ayatollah Khamenei na cewa, Birtaniya ta aikata fashin teku kuma ta sace jirginsu.

Ya ce Iran ba za ta kyale wannan muguntar ba, kuma za ta mayar da martani a lokaci da kuma wurin da ya dace.

Sojojin ruwan Birtaniya ne suka kwace jirgin dakon man Iran na Grace 1, a kusa da gabar ruwan Gibralta a farkon wannan watan, bisa zargin dakon mai zuwa Syria, wanda ya sabawa takunkumin Tarayyar Turai. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China