Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran ta yi kira ga kasashen Gulf da su hada kai don tabbatar da tsaro a tekun Fasha
2019-08-15 11:16:18        cri
Shugaba kasar Iran, Hassan Rouhani, ya bukaci kasashen dake yankin tekun Fasha, da su kulla akala a tsakaninsu, don tabbatar da tsaron sufurin teku

Rouhani wanda ya yi wannan kiran yayin taron majalisar gudanarwar kasar, ya bayyana cewa, batun kafa sabon kawance a yankin Gulf da yankin gabar tekun Oman, ba zai yi tasiri ba, ko da an aiwatar da shi, ba zai kuma taimaka wajen tabbatar da tsaron shiyyar ba.

Amurka da kawayenta sun bayyana damuwa kan yadda Iran ke kara yin tasiri a shiyyar. A kwanakin baya ne, Amurka ta kara girke dakaru, da jiragen ruwan yaki da masu kakkaba jirage a iyakokin kawayenta dake yankin Gulf, sannan ta yi kira da a kafa hadakar sojojin tsaron teku.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China