Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Faransa da Iran sun tattauna kan batun nukiliyar Iran ta wayar tarho
2019-07-08 13:43:01        cri

Fadar shugaban Faransa ta ba da sanarwa a daren 6 ga wata cewa, shugaban kasar Emmanuel Macron ya bugawa takwaransa na kasar Iran Hassan Rouhani wayar tarho don tattauna batun nukiliyar kasarsa.

Sanawar ta ce, Macron ya mai da hankali matuka kan hadari da mumunan tasiri idan an kara takaita yarjejeniyar nukiliyar Iran a duk fannoni. Kuma bangarorin biyu sun yarda da tattaunawa kan sharudan farfado da shawarwari tsakanin bangarori daban-daban masu ruwa da tsaki kafin ranar 15 ga watan nan.

Dadin dadawa, sanarwar ta ce, a 'yan kwanaki masu zuwa, Macron zai ci gaba da yin sulhunta Iran da dai sauran kasashe masu alaka don sassauta halin da ake ciki a wannan fanni. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China