Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta jaddada kira ga Amurka da ta dakatar da tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong
2019-08-06 11:12:54        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying, ta ce kasar ta na fatan Amurka za ta dakatar da tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong, tana mai cewa bai dace wani sashi ya yi wasa da matsayin Sin, na kare manufar nan ta "kasa daya tsarin mulki biyu" da take aiwatarwa ba. Kaza lika Sin za ta kare ci gaba da daidaito a yankin na Hong Kong.

Hua Chunying ta yi wannan tsokaci ne, lokacin da take maida martani game da wata wasika da wasu 'yan majalissar dokokin Amurka suka gabatarwa gwamnatin shugaba Trump, suna mai kira ga gwamnatin da kada ta goyi bayan danniya da ake yiwa masu zanga zangar lumana a Hong Kong, ta kuma yi Allah wadai da kiran masu zanga zangar da 'yan tada zaune tsaye.

Hua ta ce abu ne sananne cewa, masu tsattsauran ra'ayi a Hong Kong, sun kutsa kai da karfin tuwo cikin ginin majalissar dokokin yankin, da ginin ofishin gwamnatin tsakiya dake wurin, inda suka lalata wasu kayayyaki, suka haddasa cunkoso, da karya doka da oda, kana suka boye wasu abubuwa da makamai masu hadari.

Masu tsattsauran ra'ayin sun kuma farmaki 'yan sanda da muggan makamai, suka yi musu duka, har ma suka gutsurewa wasu 'yan yatsu. Baya ga bata tuta, da tambarin kasar da suka yi.

Jami'ar ta kara da cewa, "daukacin mutane masu tunani, za su amince da cewa, wannan mataki na amfani da karfin tuwo ya wuce matsayin wayewa. Mutane ne da suka karya tsarin zanga zangar lumana, da matsayin furta albarkacin baki. Har ila yau sun keta dukkanin dokokin yankin Hong Kong, da hurumin al'umma na zaman lafiya da tsaro, da ci gaba. Kaza lika sun tozarta manufar Sin ta kasa daya tsarin mulki biyu, wanda dukkanin su matakai ne da ko kadan Sin ba za ta amince da su ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China