Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakada Cui Tiankai: kasar Sin ba za ta laminci tsoma bakin da kasashen ketare suka yi game da batun Hongkong ba
2019-08-03 16:19:26        cri
Jiya Juma'a, jakadan kasar Sin dake Amurka Cui Tiankai, ya gabatar da sharhi a mujallar "Newsweek" ta kasar Amurka, a cikin sharhin mai taken "Tsayawa kan manufar kasa daya, tsarin mulki iri biyu, da kiyaye wadata da zaman karko na Hongkong", jakada Cui ya bada amsa kan tambayoyin da kasashen waje suka nema game da manufar ta kasa daya, tsarin mulki iri biyu.

A cikin sharhin, Cui ya ce, hadarin da yafi girma da ake fuskanta kan manufar shi ne, wasu mutane masu boyayyiyar manufa a kasashen duniya da Hongkong suna da nufin maida Hongkong a matsayin wata kofa wajen kai farmaki kan tsarin babban yankin kasar Sin, har ma tayar da rikici a duk kasar Sin baki daya.

Cui ya nuna cewa, matakan nuna karfin tuwo da aka tayar a 'yan kwanakin da suka wuce, an dauka ne ba domin batun fadin albarkacin baki da shirya tarurruka cikin 'yanci ba, sun kawo tasiri ga babban tushen doka da oda na Hongkong. Gwamnatin kasar Sin na tsayawa kan nuna goyon baya ga gwamnati da 'yan sanda na yankin musamman na Hongkong wajen daukar matakan da suka wajaba, don yanke hukunci kan wadanda suka tayar da ayyukan nuna karfin tuwo, da kiyaye zaman karko na yankin na Hongkong. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China