Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Babu wanda ya iya sa hannu a harkokin yankin Hongkong
2019-08-02 10:25:15        cri

Mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma direktan ofishin kwamitin kula da harkokin waje na kwamitin tsakiya Mista Yang Jiechi ya zanta da manema labarai game da wasu batutuwa dake shafar yankin Hongkong na baya-baya.

Ya ce, tun watan Yuni na bana, an yi ta zanga-zanga da taruka da dama kan gyaran fuska da aka yiwa "Ayar doka kan masu aikata laifi da suka gudu" da "Dokar taimakawa juna kan babban laifi", wasu masu tsattsauran ra'ayi sai suka tada zaune tsaye da gangan, har suka yi amfani da karfin tuwo, lamarin da ya kawo babbar illa ga tsaron jama'ar yankin, baya ga mummunan tasirin da ya yi ga zaman doka da oda a fannin gudanar da harkokin shari'a da zamantakawar al'umma da tattalin arziki da zaman rayuwa a yankin da kuma bata sunan yanki a duniya. Gwamnatin tsakiya na goyon bayan gwamnatin yankin da su daidaita wadannan batutuwa bisa doka.

Wajibi ne mu bayyana cewa, wasu gwamnatocin kasashen yamma ciki hadda Amurka sun mayar da fari baki kan batun gyaran fuskar da yankin na Hong Kong ya yi kan ayoyoin doka, ya kasa gane karya da gaskiya, har ya rura wuta halin da yankin ke ciki da tsoma baki yadda suke so, har manyan jami'ansu sun gana da magudun masu tada hankali a yankin, matakin da ya zuga wadannan masu tsattsauran ra'ayi a yankin da nufin keta zaman lafiya da wadata mai karko a yankin. Ko shakka babu, wadannan matakai tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma sun saba muhimman sharudan dokoki da ka'idoji na kasa da kasa game da dangantakar kasa da kasa, har ma ya kawo babbar illa ga makomar dangantakar dake kasancewa tsakanin Sin da wadannan kasashe. Sin na nuna matukar rashin jin dadi da bacin rai kuma ba za ta yarda da hakan ba ko kadan. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China