Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mahukuntan Hong Kong sun yi tir da masu zanga-zanga da suka aikata laifin nuna karfin tuwo
2019-07-15 15:43:06        cri

A daren ranar 14 ga wata, kakakin mahukuntan yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ya bayyana cewa, bayan da aka yi zanga-zangar a harabar Shatin a wannan rana da yamma, wasu masu zanga-zangar sun toshe hanyoyi da gangan, sannan suka kaiwa 'yan sanda hari, a yunkurin tayar da tarzoma. Mahukuntan Hong Kong sun yi tir da wadannan laifuka da kakkausar murya.

Lo Wai-chung, kwamishinan 'yan sanda na yankin musamman na Hong Kong ya yi bayanin cewa, a kalla 'yan sanda 10 ne sun ji rauni, kuma an kai su asibiti don yi musu jinya. A safiyar ranar 15 ga wata, Lo Wai-chung ya ziyarci asibitin da ke Tai Po domin nuna jinjinawa ga 'yan sandan da suka ji rauni. Ya bayyana bacin ransa tare da tausayawa 'yan sanda da suka jikkata. Ya kuma yi tir da lamarin da kakkausar murya. Har ila yau ya jaddada cewa, bangaren 'yan sandan zai bi bahasin lamarin baki daya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China