Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin kwamishinan ma'aikatar wajen kasar Sin a Hong Kong ya soki kalaman dan majalisar Amurka kan 'yan sandan HKSAR
2019-07-29 10:36:31        cri

Mai magana da yawun ofishin kwamishinan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin dake yankin musamman na Hong Kong, ya yi Allah wadai da kalaman da wani dan majalisar dokokin Amurka ya yi game da matakan da 'yan sandan yankin suka dauka na daidaita zanga-zangar baya-bayan da wasu matasa suka gudanar.

Kakakin ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, a shekarar 2018 da ta gabata, an ayyana yankin a matsayin na 16 a duniya wajen gudanar da harkokinsa bisa doka, matakin da ya dara na kasar Amurka, wanda ya kai matsayi na 60 a duniya a shekarar 1996.

Ya ce, 'yan siyasar kasar Amurka ba su taba yin magana a kan batun rashin 'yanci da kare hakkin dan-Adam a yankin na Hong Kong a lokacin da yake hannun Turawan mulkin mallaka ba, ko su nuna damuwa game da matsayi da ma halin da al'ummar yankin ke ciki a wancan lokaci ba.

Amma a cewarsa, yanzu 'yan siyasar Amurkar na nuna yatsa kan yankin da ke cin gajiyar 'yanci marasa iyaka, suna zargin cewa, gwamnatin kasar Sin na ci gaba da take 'yanci da ma ikon da yankin ke da su, wannan karya ce da munafarci.

Jami'in ya kuma nuna cewa, babu inda ake amfani da tashin hankali wajen neman biyan kowa ce irin bukata, don haka duk wani tashin hankali da ayyuka na saba doka a yankin, sun saba dokar tsaro da zaman lafiyar jama'a, kana hakan kalubalantar tsarin nan na "kasa daya, amma tsarin mulki biyu ne.

Ya ce, a maimakon 'yan siyasar na Amurka su amince cewa, wasu daga cikin masu boren sun saba doka, sai kawai wasu daga cikinsu da ma daidaikun kafafen yada labarai suka nace cewa, zanga-zangar da matasan suka shirya ta zaman lafiya ce, kana suka zargin 'yan sandan yankin musamman na Hong Kong da musguna musu, har ma suka yi kira ga gwamnatin yankin Hong Kong da ta sauke nauyin dake bisa wuyanta, shin wannan ba zargi ne da cin fuska da nufin zubar da kimar su ba?

A don haka, kakakin ya yi kira ga wasu 'yan siyasa na ketare da su gaggauta daina aikewa da munanan sakonni na ayyukan tashin hankali da suka saba doka, su kuma gaggauta daina furta tare da aikata duk wasu abubuwan da za su kawo nakasu ga tsarin nan na "kasa daya, amma tsarin mulki biyu", da kokarin kawo karshen tashin hankali da gurgunta makomar yankin, da gaggauta daina tsoma baki a harkokin cikin gidan yankin musamman na Hong Kong da cikin gidan kasar Sin baki daya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China