2019-08-05 10:19:53 cri |
Kakakin gwamnatin yankin musammam na Hong Kong na kasar Sin, ya bayyana a jiya cewa, zanga –zangar da ake yi a yankin a baya-bayan nan, ya zarce iyakar lumana, don haka gwamnatin da daukacin al'umma ba za su amince da ita ba.
Da yake tsokaci kan tabarbarewa zanga-zangar, kakakin ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, keta dokoki da hana al'umma kwanciyar hankali da kai hare-hare kan 'yan sanda za su illata yankin da tattalin arzikinsa da kuma zaman rayuwar jama'a.
Ya ce zanga-zangar da aka shirya domin bayyana bukatu, ta sa an kara kaimi kan toshe tituna da sauran wasu abubuwan da suka sabawa doka. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China