![]() |
|
2019-07-22 10:16:31 cri |
Kakakin ofishin harkokin Hong Kong da Macao na majalisar gudanarwar kasar Sin ya yi tir da matakin da wasu masu zanga-zanga suka dauka, na tsare kofar ofishin wakilin gwamnatin tsakiyar kasar dake yankin Hong Kong, tare da bata tambarin kasa dake kofar ofishin da wasu launuka.
Jami'in ya ce da yammacin ranar Lahadi, masu zanga-zangar sun yi wa ofishin tsinke, tare da bata bangonsa da wasu rubuce-rubuce na batanci, da kuma kokarin kutsa kai cikin ginin.
Hakan a cewar jami'in, mataki ne na kalubalantar ikon gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, ya kuma keta hurumin ginshikin nan na "kasa daya tsarin mulki biyu", wanda hakan babban al'amari ne dake nuna mummunan misali da ba za a lamunta ba. (SAMINU)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China