Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sassa daban daban na Hong Kong: taron bita kan yankin ya nuna hanyar kwantar da kura a Hong Kong
2019-08-09 10:12:20        cri

Kwanan baya, ofishin sashen kula da harkokin Hong Kong da Macao na majalisar gudanarwar kasar Sin, da kuma ofishin gwamnatin tsakiyar kasar Sin da ke yankin musamman na Hong Kong, sun shirya wani taron bita dangane da halin da ake ciki a Hong Kong a birnin Shenzhen.

A yayin taron bitar, daraktan ofishin harkokin da suka jibanci yankunan Hong Kong da Macao a majalisar gudanarwar kasar Sin Zhang Xiaoming, ya sanar da ra'ayin gwamnatin tsakiyar kasar kan yadda za a kwantar da kura a yankin na Hong Kong.

Sassa daban daban na Hong Kong suna ganin cewa, taron bitar ya nuna hanyar yadda za a kwantar da kura a yankin. Daukacin mazauna yankin za su mara wa mahukuntan Hong Kong, da kantomar yankin baya, wajen gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata, za su kuma goyi bayan 'yan sandan yankin wajen kwantar da kura, da dakile dukkan aikace-aikacen nuna karfin tuwo da sabawa doka, a kokarin maido da odar zamantakewar al'umma a yankin cikin hanzari. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China