Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Duk wani yunkuri na tsoma baki cikin al'amuran Hong Kong ba zai yi nasara ba in ji jami'ar kasar Sin
2019-08-08 10:45:29        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce duk wani yunkuri na tsoma baki cikin harkokin da suka jibanci yankin Hong Kong, da na cikin gidan kasar Sin ba zai yi nasara ba.

Hua ta bayyana hakan ne a jiya Laraba, yayin da take mai da martani ga kiran da wasu sanatocin kasar Amurka biyu suka yi, na a gudanar da bincike game da yanayin da ake ciki a yankin Hong Kong.

Jami'ar ta ce sanatocin sun gaza wajen gane fari daga baki, kuma sun kaucewa bayyanawa duniya irin mummunan tasiri dake tattare da ayyukan masu tada kayar baya, na tayar da fitina da karya doka. Ta ce maimakon hakan sun mayar da hankali kacokan ga irin matakan da 'yan sandan yankin suka dauka bisa doka, na wanzar da zaman lafiya ba tare da amfani da karfin tuwo ba, da aikin kare doka da oda da zamantakewar al'umma. Ta ce babu wata gwamnati da ta san ciwon kanta, da za ta kau da kai daga munanan irin wadannan ayyukan bata gari.

Jami'ar ta kuma kara da jan hankalin sassan 'yan siyasar Amurka masu ruwa da tsaki game da wannan lamari, da su gaggauta dakatar da goyon bayan ayyukan bata gari, su kuma daina tsoma baki cikin harkokin yankin na Hong Kong. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China