Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na adawa da duk wata kasa dake son tsoma baki game da harkokin Hong Kong
2019-07-02 20:29:27        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce Sin na adawa da duk wata kasa, dake son tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong na Sin.

Geng Shuang ya ce kutsawa da wasu suka yi, cikin ginin majalissar tsara dokokin yankin Hong Kong a jiya Litinin, tare da lalata wani sashe na kayan da ke ciki, mummunan laifi ne da ya sabawa doka da oda.

Ya ce Sin ta yi kakkausan suka game da tada tarzoma a yankin, tana kuma goyon bayan gwamnati, da 'yan sandan yankin, a yunkurin su na tabbatar da dawo da zaman lafiya bisa tanajin dokokin yankin.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin ya kuma jaddada cewa, Hong Kong yankin musamman ne na kasar Sin, kuma dukkanin wasu harkokin sa batu ne da ya shafi kasar Sin kadai.

Geng ya ce "muna matukar nuna rashin jin dadin mu, da adawa da yunkurin wasu kasashe na shiga harkokin yankin Hong Kong". Ya kuma bukaci irin wadannan kasashe, da su yi taka tsan tsan wajen furta kalamai, domin kaucewa aika wani sako da bai dace ba, ko aiwatar da wasu matakai masu cin karo da doka.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China