Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afirka ta Kudu: an yayata taron baje kolin kayayyakin shige da fice na duniya karo na 2 da za a yi a Shanghai
2019-08-05 13:10:52        cri

A karshen makon jiya ne a a birnin Pretoria na kasar Afirka ta Kudu, ofishin jadakancin kasar Sin da ke kasar, da kuma hadaddiyar kungiyar kasuwancin Shanghai a kudancin Afirka, suka yayata taron baje kolin kayayyakin shige da fice na kasa da kasa karo na 2 da za a gudanar daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwambar bana, a birnin Shanghai na kasar Sin.

Jakadan kasar Sin a Afirka ta Kudu Lin Songtian, ya bayyana a wajen taron cewa, taron baje kolin da za a gudanar a Shanghai wani muhimmin dandali ne, wanda zai kara azama ga bunkasa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ta Kudu, ta fuskar raya tattalin arziki da ciniki. Kana kuma zai samar wa kamfanonin Afirka ta Kudu kyakkyawar dama, ta tattaunawa kan gudanar da hadin gwiwar moriyar juna, da kara sanin al'adun kasar Sin. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China