Manzon musamman na shugaban kasar Sin zai halarci bikin rantsuwar Matamela Ramaphosa
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya sanar a yau Alhamis cewa, bisa gayyatar da shugaba Matamela Ramaphosa ya yi masa, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakin shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, mista Hao Mingjin, zai isa birnin Tsawane, wato Pretoria, domin halartar bikin rantsuwar shugaba Ramaphosa, wanda zai gudana a ranar Asabar mai zuwa. (Bello Wang)
Labarai masu Nasaba