Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Baje-kolin kayan saka na kasar Sin a Afirka ta Kudu zai inganta hadin-gwiwar kasashen biyu
2019-06-13 11:21:48        cri

 

An kaddamar da bikin baje-kolin kayan saka na kasar Sin karo na hudu kana da baje-kolin tufafi da takalma na kasa da kasa jiya Laraba a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu.

Karamin jakadan Sin dake Cape Town Lin Jing ya bayyana cewa, dangantakar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin Sin da Afirka ta Kudu na da matukar muhimmanci, kuma hadin-gwiwar kasashen biyu a fannoni daban-daban na kara fadada a 'yan shekarun nan. Tun da aka fara shirya bikin baje-kolin kayan saka na kasar Sin a Afirka ta Kudu a shekara ta 2016, ya zuwa yanzu, ya kara habaka har ya riga ya zama wani muhimmin dandali ga kamfanonin samar da kayan saka na kasar Sin da su raya kasuwanci a kasashen waje.

Bana, an shirya bikin baje-kolin kayan saka na kasar Sin da baje-kolin tufafi da takalma na kasa da kasa gami da bikin baje-kolin kayan Afirka a lokaci guda a Afirka ta Kudu, al'amarin dake da babbar ma'ana ga inganta sana'ar samar da kayan saka a kudancin nahiyar Afirka da karfafa hadin-gwiwar sana'o'in Sin da Afirka ta Kudu.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China