Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Afirka ta Kudu ya yi maraba da fasahar 5G ta kamfanin Huawei
2019-07-06 15:41:13        cri
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa, ya ce yana maraba da fasahar sadarwa ta 5G da kamfanin Huawei na kasar Sin ya kai kasarsa.

Shugaban ya fadi haka ne a wajen taron tattalin arziki masu alaka da fasahohin zamani da kuma juyin juya hali na masana'antu karo na 4, wanda ya gudana a Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a jiya Jumma'a.

A cewar shugaban, kamfanonin sadarwa na kasarsa sun taba rubuta masa wata wasika, inda suka bayyana cewa, idan aka toshe hanyar kamfanin Huawei ta shiga kasuwannin kasar Afirka ta Kudu, to, za a hana ruwa gudu ga kokarin kasar na kafa tsarin fasahar sadarwa ta 5G, har ma da haifar da illoli ga fasahohin sadarwa na 3G da 4G da ake amfani da su yanzu. Shugaban na Afirka ta Kudu ya ce, suna bukatar fasahar 5G, kana kamfanin Huawei ne kadai zai iya ba su fasahar. Saboda haka suna goya masa baya, tare da sa ran ganin kamfanin ya ba kasar gami da duniya baki daya, fasahohi masu inganci." (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China