Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangaren kasuwanci na Afrika ta Kudu ya yi kira ga nahiyar Afrika da ta inganta dangantakarta da kamfanonin kasar Sin
2019-07-30 10:52:19        cri
Shugaban kamfanin Futran Holdings na kasar Afrika ta Kudu, Andries Louw, ya ce wajibi ne Afrika ta Kudu da sauran kasashen Afrika, su inganta dangantakarsu da kamfanonin kasar Sin domin su bunkasa tattalin arzikinsu.

Shugaban kamfanin mai kula da aikin sufuri ya bayyana haka ne jiya a birnin Johannesburg, yayin taron baje kolin cinikayya na kasa da kasa, na bana, na Afrika ta Kudu.

Andries Louw, ya ce kasar Sin ta bude kofarta, kuma a yanzu tana ba kamfanoninta da na kasashen waje damarmaki iri guda, sannan suna neman hadin gwiwa.

Ya ce kasar Sin na neman abokan hulda a duniya, don haka kamata ya yi kasashen Afrika su inganta dangantakarsu da ita domin morar hidimominta, da fasahar zamani da ababen more rayuwa.

Mataimakin darakta Janar na hukumar kula da cinikayya da ci gaba ta ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, Jia Guoyong, ya ce Sin ta kuduri niyyar zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya.

Ya kuma yi kira ga mahalarta su yi amfani da taron wajen tattauna batutuwan kasuwanci da cimma yarjejeniyoyi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China