Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsohon shugaban Afrika ta Kudu ya bayyana a gaban kotu inda ake tuhumarsa da laifin cin hanci
2019-05-21 10:48:27        cri
Tsohon shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma, ya bayyana a gaban babbar kotun KwaZulu-Natal dake birnin Pietermaritzburg a jiya Litinin, domin fuskantar tuhume-tuhumen cin hanci.

Lauyan Jacob Zuma, Muzi Sikhakha, ya bayyanawa kotun cewa, siyasa ce ta ingiza shari'ar da ake wa wanda yake karewa, don haka ya kamata a kori karar.

Dandazon jama'a ne suka taru a wajen kotun domin nuna goyon baya ga shugaba Zuma.

A watan Maris na bara ne hukumar shigar da kara ta kasar NPA, ta sake gabatar da tuhumar cin hanci akan Zuma, tuhumar da aka rufe a farkon shekarun 2000, lamarin da ya ba Zuman damar zama shugaban kasar a shekarar 2009.

Tuhume-tuhumen na da alaka da yarjejeniyar cinikayyar makamai da darajarta ta kai biliyoyin kudin rand da kasashen Turai a karshen shekarun 1990, tuhumar da Zuma ya musanta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China