Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manzon musamman na Xi Jinping ya halarci bikin kama aiki na shugaban Afirka ta Kudu
2019-05-26 17:03:25        cri
Manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shine mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar, Hao Mingjin, ya halarci bikin kama aiki na shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa jiya Asabar a birnin Tshwane, inda ya kuma yi shawarwari da shi.

Hao ya isar da sakon gaisuwa da fatan alheri na shugaba Xi Jinping zuwa ga Cyril Ramaphosa, inda ya ce, shugabannin kasashen biyu sun kawowa juna ziyara a bara, al'amarin da ya kafa alkibla ga bunkasuwar dangantakarsu bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni. Kasar Sin na fatan karfafa mu'amala da tuntuba da kasar Afirka ta Kudu, a kokarin zurfafa hadin-gwiwarsu zuwa wani sabon matsayi.

A nasa bangaren, Cyril Ramaphosa ya godewa shugaba Xi Jinping saboda tura wani babban wakilinsa don halartar bikin kama aikinsa, inda ya bayyana cewa, alakar dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudu, alaka ce ta musamman, shi da shugaba Xi Jinping dukkansu suna da babban nauyi na kara samar da zaman jin dadi ga jama'ar kasashensu, haka kuma yana fatan yin kokari tare da Xi Jinping don bude wani sabon babi ga dangantakar Sin da Afirka ta Kudu.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China