Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar FIFA za ta ziyarci Najeriya a shirye-shiryen tsara gasar cin kofin duniya ta mata
2019-08-05 10:36:34        cri
Nan gaba a yau Litinin ne ake sa ran tawagar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, za ta sauka a birnin Lagos dake kudancin Najeriya, a shirye-shiryen tsara gasar cin kofin duniya ta mata wadda kasar za ta karbi bakunci a shekarar 2020.

Jami'an na FIFA za su shafe kwanaki 4 suna duba wurare da kayayyakin wasa da ake bukata, domin gudanar gasar ta kwallon kafar mata 'yan kasa da shekaru 20 da haihuwa.

Cikin wata sanarwa da hukumar kwallon kafar Najeriya ta fitar, kuma kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu a kwafinta, kakakinta Ademola Olajire, ya ce Najeriya ta tanaji ababen da ake bukata domin gasar a biranen Lagos, da Benin, da Asaba da Uyo, domin gasar da kungiyoyin kasashe 16 za su buga.

Bayan sauka Lagos da yammaci, tawagar za ta kuma isa birnin Abuja a ranar Alhamis, domin tattaunawa da manyan jami'an ma'aikatar matasa da wasanni ta kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China