Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakarun tsaron Najeriya sun hallaka mutane 5 da ake zargi da muggan laifuka a arewacin kasar
2019-07-29 09:31:49        cri
Rundunar sojojin Najeriya ta sanar a ranar Lahadi cewa ta kashe wasu mutane 5 kana ta damke wasu mutane 4 wadanda ake zargi da aikata muggan laifukan garkuwa da mutane da fashi da makami da kuma addabar jama'a a jahar Kaduna dake arewacin kasar.

Ezindu Idimah, kakakin rundunar sojojin kasar ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce 'yan bindigar an hallakasu tare da damke wasu daga cikinsu ne yayin aikin sintirin da jami'an tsaron suka kaddamar a karo 2 a yankunan Chikun da Igabi dake jahar a ranar Laraba.

Wasu daga cikin bata garin sun tsere da raunukan harbin bindiga a jikinsu, haka zalika jami'an tsaron sun yi nasarar ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su a ranar Alhamis.

Idimah ya ce an kwato wasu makamai da albarusai daga wajen 'yan bindigar.

Jahar Kaduna tana daya daga cikin jahohin dake fama da matsalar masu garkuwa da mutane da hare-haren 'yan fashi da makami musamman a 'yan watannin da suka gabata.

Gwamnatin Najeriya ta sha kaddamar da ayyukan tsaro na musamman masu yawa da nufin kawo karshen matsalar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China