Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan sandan farin kaya sun tabbatar da kama tsohon dan takarar shugaban kasa a Nijeriya
2019-08-05 10:02:10        cri

'Yan sandan farin kaya sun tabbatar da kama Omoyele Sowore, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta African Action Congress wato AAC da sanyin safiyar ranar Asabar.

Kakakin 'yan sandan Peter Afunanya, ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa, an kama dan siyasar ne saboda kiran da ya yi na kifar da gwamnati a Nijeriya.

Peter Afunanya ya ce, 'yan sanda na zargin yana mu'amala da wasu daga kasashen waje da nufin haifar da rikici a Nijeriya.

A cewar rahotanni daga kafafen yada labarai na kasar, Omoleye Sowore, wanda ya tsaya takaran shugabancin kasar a zaben 2019 kuma ya sha kaye, ya shirya jagorantar zanga-zangar kifar da gwamnati a Nijeriya daga yau Litinin. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China