Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi Allah wadai da kisan mutane da aka yi a arewa maso gabashin Nijeriya
2019-07-30 10:04:29        cri

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres da shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar UNHCR, Filippo Grandi, sun yi Allah wadai da kisan mutane 65 da ake zargin mayakan BH da aikatawa a arewa maso gabashin Nijeriya.

Cikin wata sanarwa, Antonio Guterres ya yi kira da a kawo karshen hare-hare kan fararen hula, yana mai tabbatar da cewa irin wadanan hare-haren babbar barazana ce ga tsaron bil adama, kana suna keta dokokin jin kai na kasa da kasa.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Tweeter a ranar Lahadi, Shugaban hukumar UNHCR Filippo Grandi, ya bayyana harin a matsayin kisan kiyashi, yana mai cewa rashin tsaro na ci gaba da jefa fararen hula cikin mawuyacin hali a yankin, ciki har da mutane miliyan 2 da suka rasa matsugunansu da kuma masu neman mafaka a kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China