Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nutsewar kwale kwale ta sabbaba rasuwar mutane 15 a Najeriya
2019-08-01 21:27:25        cri
A kalla gawawwakin mutane 15 ne aka tsamo daga ruwa, bayan da wani kwale kwale da suke ciki ya nutse a kogin Malale dake jihar Niger, a shiyyar tsakiyar Najeriya.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta kasar reshen jihar Niger Ibrahim Inga, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kwale kwalen na dauke ne da fasinjoji 50, dake kan hanyar su ta zuwa cin kasuwa lokacin da ya kife a ranar Asabar.

Kaza lika jami'in ya ce kalubalen sadarwa, ya sanya jami'an aikin ceto gaza isa wurin a kan lokaci, inda sai ma da yammacin Talata ne suka samu labarin aukuwar hadarin, daga nan ne kuma aka fara aikin laluben wadanda suka nutse.

Ya zuwa ranar Laraba, jami'in ya ce gawawwakin mutane 15 kadai aka iya tsamowa. An kuma ci gaba da aikin laluben karin mutanen har zuwa safiyar ranar Alhamis din nan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China