Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe mayakan BH 10, yayin da dakarun kawance na kasa da kasa suka dakile wani hari a Nijeriya
2019-07-30 09:32:43        cri
An kashe mayakan BH 10 da safiyar jiya Litinin, yayin da dakarun kawance na kasa da kasa suka dakile yunkurin mayakan na kai hari wani sansanin soji dake garin Baga na jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya, wanda kuma ke yankin tafkin Chadi.

Sanarwar da kakakin rundunar kawancen Col. Timothy Antigha ya fitar, ta ce soja guda ya rasa ransa yayin musayar wuta da suka yi da mayakan. Kana wasu sojojin 5 sun ji rauni.

Dakarun kawancen sun hada da na kasashen Nijeriya da Chadi da Kamaru da kuma Benin.

A cewar Kakakin, rundunar za ta ci gaba da hada gwiwa da jami'an tsaron kasar wajen ci gaba da daukar matakan da suka wajaba na tabbatar da cimma burinta a yankin tafkin Chadi.

Ya ce za su kara matsa kaimi ta yadda ayyukansu zai hada da kai samame, da kwanton bauna da sintiri domin fatattakar 'yan ta'adda daga tungarsu a yankin tafkin Chadi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China