Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnan jihar Borno a Nijeriya, ya yi kira da a tura karin jami'an tsaro jihar
2019-08-02 10:47:42        cri

Gwamnan jihar Borno na yankin arewa maso gabashin Nijeriya mai fama ayyukan 'yan tada kayar baya, Babagana Zulum, ya yi kira da a tura karin jami'an tsaro jihar, domin gaggauta aikin samar da zaman lafiya a yankunan dake fama da tashin hankali.

Gwmanan ya yi kiran ne jiya a kauyen Jakana, biyo bayan harin da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram da kai wa kauyen a ranar Talata, inda suka sace mutane biyu tare da yin awon gaba da kayayyakin abinci.

Babagana Zulum, ya yi kira ga mutanen kauyen da kada su tsere saboda fargabar ayyukan 'yan ta'addan, yana mai tabbatar da cewa sojoji na kokarin shawo kan lamarin.

Kauyen Jakana na da nisan kilomita 40 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Har ila yau, Gwamnan ya ce gwamnatin jihar na duba yiwuwar sake bude ofishin 'yan sanda a kauyen domin inganta tsaron rayuka da dukiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China