Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mayakan BH sun kashe mutane akalla 55 a wani hari da suka kai arewa maso gabashin Nijeriya
2019-07-29 09:18:53        cri

Akalla kauyawa 55 aka kashe, a wasu hare-hare 3 mabambanta, wadanda mayakan Boko Haram suka kai a baya-bayan nan a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, hare-haren sun auku ne da safiyar ranar Asabar, a yankin karamar hukumar Nganzai ta jihar.

Gwamnan wanda ya kai ziyarar jaje yankin a jiya, ya ce kawo yanzu, gawarwaki 55 aka samu na mutanen kauyukan Badu Malam Kyariri da na Zawa da na Lamisula Bukar Bulala.

Shugaban 'yan sintiri na Civillian JTF dake yankin Abbagana Ali, ya ce wasu daga cikin wadanda suka mutu sun je jana'iza ne a makabarta.

Ya shaidawa wakilin Xinhua cewa, an gano kimanin gawarwaki 26 na masu jana'iza a makabartar kauyen Badu Malam Kyariri, inda ya ce sun je jana'iza ne a lokacin da aka kai harin.

Ya ce mayakan sun shiga kauyen ne cikin manyan motocin soji masu sulke 5 da aka kafa musu bindigogi masu kakkabo jirgin sama. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China