![]() |
|
2019-08-02 10:28:32 cri |
A yayin taron kara wa juna sani kan yadda za a iya taimakawa ayyukan fama da talauci ta hanyar intanet da ba da hidimar sadarwa da aka shirya a jiya Alhamis a birnin Dunhuang, babban injiniya na ma'aikata mai kula da harkokin masana'atu da sadarwa ta kasar Sin Zhang Feng ya bayyana cewa, hidimar sadarwa da aka bayar ta taimakawa jama'ar wadanda suke zaune a kauyukan dake nesa da birane da su ci gajiyar samun horo, da samun jinyya da yin kasuwanci a kan intanet da dai sauransu. Ya zuwa yanzu, yawan kauyukan dake da intanet a kasar Sin ya kai fiye da kashi 98 cikin dari, kuma saurin kama intanet a kauyuka daidai yake da na birane. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China