![]() |
|
2019-08-01 09:51:08 cri |
Mr Li ya bayyana hakan ne, yayin zaman majalisar gudanarwar kasar na jiya Laraba da ya jagoranta. Ya ce, majalisar ta gano karin matakan bunkasa kayayyakin amfanin jama'a a bangaren al'adu da yawon shakatawa, ta yadda za a biya bukatansu wadda daga karshe za a kara cin gajiyar damammakin dake cikinsu.
Ya ce, kara yawan kayayyakin bukatun jama'a ba karamin aikin ba ne, da karfafa rawar da hakan zai taka wajen bunkasa tattalin arziki, da daidaita yanayin kasuwannin cikin gida ta hanyar samar da sabbin kayayyaki masu inganci.
Firaminista Li ya bukaci sassan gwamnati, da su kara ba da jagoranci tare da bullo da manufofi, da karin matakai da za su bunkasa harkokin kasuwanci, da samar da yanayin da ya dace ga abokan cinikayyarsu.
Alkaluma na nuna cewa, a watanni na shida na farkon shekarar bana, kayayyakin da kasar ta sayar ya kai Yuan triliyan 19.5. kwatankwacin dalar Amurka triliyan 2.83. Kayayyakin bukatan jama'a ya ba da gudummawar da ta kai kaso 60.1 cikin 100 na bunkasar GDPn kasar, ya kuma ci gaba da zama ginshikin ci gaban tattalin arzikin kasar. (Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China