Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala shawarwarin tattalin arziki da kasuwanci tsakanin manyan jami'an Sin da Amurka kamar yadda aka tsara
2019-08-01 16:40:06        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya bayyana yau Alhamis cewa, shawarwarin tattalin arziki da kasuwanci zagaye na 12 da aka kammala tsakanin manyan jami'an kasashen Sin da Amurka ya kunshi wasu muhimman fannoni biyu. Na farko, yadda za'a waiwayi baya, wato a gaskata ra'ayoyi kan batun tattalin arziki da kasuwanci. Na biyu shi ne, mataki na gaba, wato a tabbatar da manufofi da hanyoyin da za'a yi wajen gudanar da shawarwari masu zuwa.

Gao ya ce, bangarorin Sin da Amurka sun nuna sahihanci tare da cimma nasarori da dama a shawarwarin wadanda aka kammala kamar yadda aka tsara. Kana a watan Agustan bana, za su kara zurfafa shawarwarin.

Har wa yau, Gao ya ce, tun daga ranar 19 ga watan Yulin bana, akwai wasu kamfanonin kasar Sin, ciki har da na gwamnati da masu zaman kansu, wadanda suka fara neman farashin wasu nau'o'in amfanin gona daga 'yan kasuwar Amurka, ciki har da wake da auduga da dawa da sauransu, kana kuma wasunsu sun riga sun sayi wasu amfanin gonar daga 'yan kasuwar Amurka.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China