![]() |
|
2019-08-01 09:32:12 cri |
Tsarin raya harkokin sufuri na yanar gizo da ma'aikatar sufurin kasar ta fitar, ya nuna cewa, kasar Sin ta lashi takwabin fito da wani tsari na zamani don bunkasa sashen sufurin kasar da sauran sassa masu nasaba.
Kamar yadda tsarin ya bayyana, za a bullo da wata manhaja, wadda za ta inganta hidimomin sufuri ta hanyar baiwa kwastomomi managartan hidimomi a duk tsawon bulaguron da suke yi.
Bugu da kari, kasar Sin za ta kara samar da wasu hidimomin jigilar kayayyaki na bai daya da karfafawa jama'a gwiwar amfani da manhajar Intanet plus a wannan fanni.
Nan da shekarar 2035, kasar Sin na fatan bullo da tsarin intanet da zai kadare dukkan bangarori gami da ababan more rayuwa na sufuri, da kula da tashi da saukan jiragen sama da motoci da samar da cikakken tsari na hidima da zai dace da zamani.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China