Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude shawarwarin tattalin arziki da cinikayya karo na 12 tsakanin Sin da Amurka
2019-07-31 20:31:29        cri
Mataimakin firaministan kasar Sin Liu He, da wakilin Amurka a fannin cinikayya Robert Lighthizer, da kuma sakataren baitulmalin Amurka Steven Mnuchin, sun gudanar da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya a karo na 12 tsakanin Sin da Amurka a birnin Shanghai na kasar ta Sin. Zaman dai ya gudana ne tsakanin ranekun Talata da Laraba.

Mataimakin firaministan kasar Sin Liu He, wanda kuma mamba ne a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, shi ne ya jagoranci bangaren Sin a yayin shawarwarin.

Bisa matsaya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a taron G20 da aka yi a birnin Osaka, wakilan sassan biyu sun yi tattaunawa ta hakika, cikakkiya, mai zurfi kuma mai ma'ana. Sun kuma yi musayar yawu game da muhimman batutuwa da suke maida hankali a kai a sassan tattalin arziki da cinikayya.

Kaza lika bangarorin biyu sun tattauna game da kara yawan hajojin amfanin gona na Amurka da ake shigarwa kasar Sin, bisa bukatar kasuwannin kasar, da ma kyakkyawan yanayin da Amurka za ta samar domin shigar da hajojin.

Bugu da kari, sassan biyu za su sake gudanar da shawarwarin a karo na gaba, cikin watan Satumbar dake tafe a kasar Amurka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China