An bude shawarwarin tattalin arziki da cinikayya karo na 12 tsakanin Sin da Amurka
Mataimakin firaministan kasar Sin Liu He, da wakilin Amurka a fannin cinikayya Robert Lighthizer, da kuma sakataren baitulmalin Amurka Steven Mnuchin, sun gudanar da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya a karo na 12 tsakanin Sin da Amurka a birnin Shanghai na kasar ta Sin. Zaman dai ya gudana ne tsakanin ranekun Talata da Laraba.
Mataimakin firaministan kasar Sin Liu He, wanda kuma mamba ne a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, shi ne ya jagoranci bangaren Sin a yayin shawarwarin. (Saminu)