![]() |
|
2019-07-31 14:12:20 cri |
A cewar daftarin, za a samar da tallafin kudi ga aikin gina sabbin filayen kwallo da fadinsu ke daukar 'yan wasa 11-11 a kowanne bangare da Yuan miliyan 2 kowanne, kwatankwacin dala 290,600. Sannan game da sabbin filaye masu daukar 'yan wasa 5-5 da masu daukar 7-7 a kowannen bangare, gwamnatin kasar za ta ba da kudin Yuan miliyan 1 bisa kowannensu. An gabatar da matakin ne domin masu kaunar kwallon kafa su samu saukin samun ingantattun filayen kwallo, tare da rage kudaden da suke kashewa. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China